1 Peter 1

1Wasiƙa daga Bitrus, manzon Yesu Kiristi,

Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a cikin duniya, da suke warwatse koʼina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,
2waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa:

Alheri da salama su zama naku a yalwace.

Yabo ga Allah domin Bege Mai Rai

3Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba—ajiyayye a sama dominku, 5ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yǎ zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne-wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta-domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.

10Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da zata zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse, 11suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa saʼad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za ta bi. 12Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, saʼad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku waʼazin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko malaʼiku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

Ku Zama Masu Tsarki

13Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku saʼad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14Kamar ʼyaʼya masu biyayya, kada ku bi mugayen shaʼawace-shaʼawacen da dā kuke da su saʼad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15Sai dai kamar yadda wanda ya kira ku mai tsarki ne, haka ku ma ku kasance masu tsarki a cikin dukan ayyukanku; 16gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
L Fir 11.44, 45; L Fir 19.2; L Fir 20.7


17Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shariʼa bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

22Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ʼyanʼuwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24Gama,

“Dukan mutane kamar ciyawa suke,
darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;
ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
25amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”
Ish 40.6-8

Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku waʼazi.

Copyright information for HauSRK